Matashi Ya Mutu A Tsaka Da Kece Raini Da Budurwansa.
Matashi ya ce ga garinku yayin da yake tsaka da nuna kurewarsa yayin kwanciya da wata abokiyar sharholiyarsa
Budurwar tasa da makwabta sukaga lokacin da ya shiga da ita daki ta tsere bayan ganin halin da ake ciki
Bincike ya nuna maganin kara karfin maza ya sha domin an gano sauransa a cikin dakinsa da wasu lemukan kara kuzari
Wani mai aski wanda aka ambata da suna Otubong ya mutu bayan zargin kwanciya da abokiyar sharholiyarsa a yankin Mile 2 da ke Port Harcourt, jihar Ribas, a ranar Juma’a.
Jaridar Punch ta rahoto cewa an ga mutumin a yammacin ranar Alhamis yana shiga daki da budurwar a yankin da ke da cunkoson jama’a.
An kuma tattaro cewa mutumin mai matsakaicin shekaru ya sha wasu magungunan kara kuzarin maza, ciki harda wani barasa.
Sai dai kuma, a safiyar ranar Juma’a, daya daga cikin makwabtansa da ya shiga duba shi ya tarar da kofarsa a bude.
Makwabcin ya ce da safen nan (Juma’a) ne daya daga cikin makwabtansa ya je karbar abu a gidansa sai ya ga cewa kofar a bude take.
“Ya ce bayan ya kwankwasa tare da kiran sunansa ba tare da an amsa masa ba sai kawai ya yanke shawarar shiga ya ga mutumin.
“Don haka sai ya fasa ihu sannan nan take ya fito ya sanar da sauran mazauna yankin abun da ya gani. Sai mutane suka fito, suka dauke shi sannan suka kai rahoton lamarin wajen yan sanda.”
A halin da ake ciki, wata majiya ta yan sanda ta sanar da manema labarai cewa an gano lemun kara kuzari biyu, fakitin tramadol biyu da wani maganin kara karfin maza a dakinsa, rahoton Within Nigeria.
Lamarin ya ja hankalin mazauna unguwannin da ke kusa, wadanda suka je tabbatar da abun da suka ji kafin a kai rahoton lamarin ofishin yan sanda na Azikiwe a Port Harcourt.
Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar yan sandan jihar Ribas, Grace Iringe-Koko, ba domin bata amsa kiran wayar da aka yi mata ba a daidai lokacin kawo wannan rahoton.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.