Matashi Ya Yanke Soyayya Saboda Maitan Madaran Hollandia Da Budurwan Ke Yi.
Wata hira tsakanin wata budurwa yar Najeriya da wani saurayi wanda ta ke burgewa ta janyo cece-kuce a Twitter.
Matashin ya shigar da bukatarsa a wajen budurwar amma ita hankalinta ya fi karkata wajen cinye masa dukiya.
Masu amfani da yanar gizo sun bayyana mabanbanta ra’ayoyi kan hirar wacce ta karade shafin inda wasu suka yi ta caccakarta
Wata budurwa yar Najeriya ta sha suka sosai a yanar gizo bayan hirar da ta yi a Twitter da wani matashi da ya nuna yana ra’ayinta ta bayyana.
Matashin ya yi mata magana ta DM domin gaya mata cewa yana ra’ayinta sannan ya bukaci da ta ba shi lambar waya.
Sai dai, budurwar a cikin amsar da ta ba shi, ta bukaci sai ya nemi cancantar samun lambarta ta hanyar siyo mata shawarwa da abin sha mai suna Don Simon.
Ta kuma ci gaba da bukatar sai ya siyo wa kawarta Hollandia yoghurt duk lokacin da suka amince cewa za su fita yawon hira.
Hirar ta su dai ta tayar da kura a yanar gizo, inda mutane da dama musamman maza suka caccaketa bisa wannan bukatu da ta zayyano.
A yayin da yake sanya hirar ta su, matashin wanda ya fusata ya kira budurwar da ‘mara kunya.’
Masu amfani da yanar gizo sun yi martani bayan budurwa ta nemi wasu abubuwa a hannun saurayi.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.