Matashiya Mai Mazaje 2 Ta Ce Suna Biya Mata Bukatunta Daban-Daban .
Wata Matashiya mai maza biyu ta bayyana dalilin auran Maza biyu Carl da Tiger sun kasance mazajen Kenya wacce ke matukar son yin soyayya da mutum fiye da daya kuma tana neman karin mazaje
Kenya da mijinta na farko Carl sun shekara 12 da aure kafin suka yanke shawarar shigo da Tiger rayuwar aurensu.
A cewar Kenya, wani bangare na rayuwarta da ya shafi tunani ya yi daidai da Carl yayin da daya bangaren da ke son jindadi da sharholiya ya yi daidai da Tiger.
Yayin da wasu matan ke neman kyawawan jaruman maza da za su kira da nasu, Kenya ta rigada ta mallaki zaratan maza har guda biyu wadanda suke mallakinta.
Kenya da mijinta na farko, Carl, sun shafe shekaru 12 da aure lokacin da ta fada tarkon son wani santalelen saurayi mai suna Tiger kuma ta gabatar da shi a rayuwar aurensu.
“Ni da Carl mun yanke shawarar cewa zan auri namiji fiye da daya saboda na hadu kuma na fada tarkon son wani gaye,” in ji Kenya.
“Mun yanke shawarar yin magana kan haka, muna al’ajabin mai ya kamata mu yi, yaya za mu bi da lamarin?” Carl ya tambaya.
“Mun tattauna kan haka tsawon shekaru sannan muka fahimci maganganun mata, za ka ga cewa ya zama dole ka bar mata su fadi abun da ke ransu sannan su zamo masu yanci,” in ji Carl.
Kenya da Tiger sun hadu a wani liyafa sannan suka fara rawa sai kuma Tiger ya yanke shawarar bibiyarta.
“Ina da abubuwan ban mamaki, Ina ji kamar Carl ya yi daidai da wani bangare nawa; da ya shafi tunani, kuma muna irin tattaunawar nan mai zurfi sannan daya bangaren shine son jin dadi, sharholiya, tafiye-tafiye kuma a nan ne muka dace da Tiger. Ni dukka mutanen biyu ce, Ina son mallakar abokan rayuwa da yawa,” in ji Kenya a shafin ET na YouTube.
Su dukka ukun suna da abubuwa na musamman a tattare da su kuma suna tallafawa junansu.
“A shirye nake na tallafawa Tiger da Kenya a duk lokacin da suke bukatar haka a soyayyarsu ko ma a wani abu na daban,” in ji Carl.
A cewar Tiger, mutane da dama na mamakin dalilin da zai sa namiji ya yarda da wani namijin a gidansu amma sun yarda da hakan domin suna kallonsa a matsayin abu mai kyau.
“Akwai dadi, duk muna son kulawa da karfi,” in ji Kenya.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim