Matata Ta Cika Kyau, Tsoro Nake Wani Ya Dauke Ta” Miji Ya Nemi Kotu Ta Rabasu
Wani magidanci san kimanin shekaru 40 a duniya ya garzaya Kotu ta raba aurensa da matarsa saboda kyaunta ya cika yawa
Mista Anold, ya fada wa Kotun cewa babu macen da ta kai matarsa kyau a fadin garinsu, yana tsoron wasu su ja hankalinta
Alkali ya bayyana cewa bai taba haduwa da Kes irin wannan ba, ya yanke hukuncin kan lamarin
Wani magidanci ya shaida wa Kotu cewa ba ya bukatar tarayya da matarsa, Hilda Mleya, yar kimanin shekara 30 a duniya saboda ta cika kyau.
Tribune ta tattaro cewa mutumin mai suna, Arnold Masuka, dan shekara 40 a duniya, ya yi wannan ikirarin ne a gaban Kotun yanki da ke garin Lusaka na kasar Zinbabwe.
A cewar Mista Anold, yana rokon Kotu ta datse igiyoyin auransa da matarsa saboda tsananin kyaun da Allah ya bata, wanda ke hana shi sukuni da rashin bacci.
Ya ce yanayin ya yi muni har ta kai ga yana fargabar tafiya wurin aiki ya barta ita kadai a gida saboda tsoron wani daban ka iya zuwa ya kwace masa ita.
Arnold ya dauki matakin garzayawa Kotu ta raba aurensa ne saboda ya gano cewa matarsa ta fi kowace mace kyau a lungu da sakon garin Gikwe na kasar Zimbabwe.
Bugu da kari, a bayanan da ya gabatar wa Kotu, ya ce matarsa tana da yawan murmushi a kowane lokaci kuma idan ta yi yana kara mata kyau.
Amma a cewarsa, abinda yake tsoro da dar-dar a cikin zuciyarsa, irin wannan murmushin da baya rabuwa da fuskarta ka iya jan hankalin wasu maza, su zo su raba shi da ita.
Alkali Chenjerai Chireya, ya bayyana cewa wannan ne karo na farko da yake jagorantar shari’a makamanciyar wannan.
Da yake yanke hukuncin kan batun, Mista Chireya, ya bukaci iyayen miji da matar su sa baki, su sulhunta ma’auratan domin samun nutsuwa da zaman lafiya a tsakaninsu.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim