Matatar Man Dangote za ta iya biyan bukatun Yan Najeriya gaba daya – Masana
Masana da yawa sun yi tsokaci a kan Matatar Man Dangote za ta iya biyan bukatun Yan Najeriya a bangarori da dama.
Tin da farko, a shekarar 2017 aka fara aikin gina Matatar Man Dangote, wadda ita ce mafi girma a Nahiyar Afirka.
A ranar 22 ga Mayu 2023, mako guda kafin saukar Shugaba Muhammadu daga mulki, ya kaddamar da matatar, wadda babban attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya gina a kan kudi Dala biliyan 19 (Naira triliyan 8.7).
Ga abubuwan 12 da ya kamata ku sani game da matatar a takaice:
Tana da karfin samar da tataccen mai ganga 650,000 a kullum.
Ita ce irinta (mai samar da ganga 650,000 a wuri guda) mafi girma a duniya.
Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) ke da kashi 20% na hannun jarin matatar.
Tattaccen man da za ta samar zai iya biyan bukatar Najeriya gaba daya.
Za ta rika fitar da tataccen mai zuwa kasashen Afirka 12.
Za ta samar da kashi 36% na tataccen man da ake bukata a Afirka.
An gina ta a yankin Ibeju-Lekki, kuma fadinta ya kai hekta 2,635.
Ana hasashen za ta samar da Dala biliyan 21 — Naira tiriliyan 9.7 — a shekara
Tana da tankuna guda 177, wadandan za su ci jimillar lita biliyan 4.742.
An horas da injiniyoyi 900 a kasashen waje kan aikin matatar mai.
Za ta iya danyen mai wasu kasashen Afirka da Gabas ta Tsakiya da Amurka.
Ta cika ka’idojin Bankin Duniya da Tarayyar Turai da hukumar DPR na takaita fitar da gurbataciyar iska.