Matsalar Tsaro: Ansanya Dokar ta baci a karamar hukumar Dandume jihar Katsina.
Daga Jamilu Garkuwan Dan-dutse Dandume
Jaridar alfijir Hausa ta samu labarin cewa Hukumomin dake kula da tsaro a karamar hukumar Dandume sun sanya dokar hana Mata sanya Hijabi tun daga karfe Shidda na yamma, haka zalika an hana Maza fita tun daga karfe Takwas na dare. Zuwa wayeyar Gari.
Wannan doka ta biyo bayan la’akarin da a kayi cewar masu garkuwa da mutane na amfani da Hijabai wajen shigowa garin domin yin garkuwa da mutane ta wannan sigar, hakazalika suna amfani da lokacin da jama’a ke jirga jigar suna yaudarar mutane suna yin abinda suka ga dama, don haka hukuma ta sanya wannan dokar akan hakan, yakamata al’umma su bada hadin kai domin samar da mafita akan wannan matsalar.
Idan mutum yayi kunnen kashi zai fuskanci fushin hukuma, Allah ya Kyauta Allah ya kawo karshen wannan masifar ameen