Mawakin Najeriya Naira Marly Ya Shwarci Musulmi da su guji aikata Alfasha a Ramadan.
‘A bar yin fare da azumi’ Naira Marley ta yi wa Musulmai nasiha akan Ramadan
Fitaccen mawakin nan na Najeriya, Azeez Fashola, wanda aka fi sani da Naira Marley, ya shawarci ‘yan’uwansa Musulmi da su guji yin caca a cikin watan Ramadan.
Mawakin ya bayyana haka ne ta wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda ya gargadi dan uwansa musulmi da ya daina caca.
Ya kuma shawarce su da su guji yin fare a kan wasanni a wannan wata mai albarka, yayin da ya kuma gargade su da yin cikakken ibada.
Watan Ramadan shi ne wanda aka saukar da Alkur’ani a cikinsa ya zama tushen shiriya ga mutane. A cikinsa akwai koyarwar gaskiya da tafarki madaidaici, da ma’auni na yin hukunci da gaskiya da qarya.‛ 2:185.