Mawallafin TikTok Bartende Ya Yi Karyan Mutuwarsa.
Wani magidanci mai shekaru 45, David Baerten, a Belgium, ya yi karyar mutuwarsa, sannan ya isa wurin binne Gawar tasa cikin jirgi mai saukar ungulu don koya wa iyalinsa darasi game da tuntuɓar juna.
Baerten, wanda ya kirkiro TikTok, ya sanar da matarsa da ’ya’yansa , kun su taimaka masa ta hanyar sanya shi a shafukan sada zumunta, a cewar Daily Mail ranar Laraba.
Daya daga cikin ‘ya’yan nasa ta yaudari mabiyan mahaifinta na dandalin sada zumunta don su yarda da mutuwarsa ta rubuta kamar haka “Ka huta lafiya, Baba. Ba zan taba daina tunanin ku ba. “Me yasa rayuwa bata da adalci haka? Me yasa ka? Za ka zama haka, kuma har yanzu kana da dukan rayuwarka a gabanka. Ina son ka Muna son ka! Ba za mu taba mantawa da kai ba.”
Bayan sanar da hakan Iyalin sun shirya gudanar da jana’izar, lokacin da masu zaman makoki suka taru, sai ga Baerten ya isa da helikwafta tare da wasu daga iyalinsa.
Baerten ya bayyana abin da ya aikata, yana mai cewa ya yi haka ne domin ya ga yadda danginsa za su yi bayan sun samu labarin mutuwarsa Ya ce, “Abin da nake gani a cikin dangina yakan cutar da ni.
Ba na samun gayyatar zuwa wani abu. Babu wanda ya ya ke nanmu. Mun girma dabam. daban batare da sanin juna ba. “Shi ya sa na sa a yada domin koyawa muku darasi na rayuwa kuma na nuna musu cewa kada ku jira har sai wani ya mutu zaku rika kai masa ziyara
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.