Meyasa kuke kashe kiristoci a Nijeriya Trump ya tambayi gwamnatin Shugaba Buhari.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace, wasu mutane suna fakewa da addini domun ciyar da tattalin arzikinsu da kuma ciyar da siyasa gaba, kuma ana bukatan cigaba da neman ilmi domin kada dinbin jama’a su kasance cikin rudani.
Shugaban yayi magana ne Nuakchott Mauritania, a ranan talata yayin da yake ganawa da Rashad Hussain jakadan Amurka mai kula da ‘yancin addini na kasa da kasa.
Da yake bada labarin ganawan sirri da yayi da tsohon shugaban kasan Donald Trump a fadan White House, shugaban na nijeriya ya tuna da Trump ya tambaye shi cewa, meyasa kuke kashe kiristoci, a nijeriya yaci gaba da shaida mishi cewa al’amarin da ke faruwa a kasan bai shafi addini ba.
Yace maimakon aikata laifuka da kuma amfani da addini da wasu keyi don cimma muradin tattalin arziki ko kuma siyasa.
Matsalace da nijeriya ta dade tana fama da ita, kuma ba lallai bane, inji shugaba Buhari, wasu mutane na amfani da addini a matsayin ra’ayi amma tare da isassen ilmi,yawancin mutane suna son yin addinin sune kawai ba tare da wata matsala ba amma wasu mutane suna samun rashin fahimtan addini don biyan bukatunsu.
Akwai abubuwa da yawa da zamu iya yi tare don inganta zaman lafiya, da kuma inganta hadin kai
Munason abunda kukeyi kuma zamuyi farin cikin taimaka muku yadda ya dace inji shi.
Rahoto Hajiya Mariya Azare.