Wata mata mai suna Maryam Abdullai ta garzaya wata kotu mai daraja ta daya da ke Kubwa a Abuja, babban birnin tarayya Abuja tana neman a raba aurenta da mijinta Ahmed Mohammed saboda rashin soyayya.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ta ruwaito, Maryam ta shaida wa kotun cewa ta auri Ahmed ne a shekarar 2003 kamar yadda dokar Musulunci ta tanada, kuma aurensu ya albarkaci ‘ya’ya hudu.
“Babu jima’i tsakanina da mijina tsawon wata tara kuma baya kula da ‘ya’yanmu. Bisani Ya bar gidan a shekarar 2020 na tsawon watanni bakwai kuma a shekarar 2021, ya shafe watanni 10 yana jinya yana cewa zan kashe shi,” in ji ta.
Maryam ta bukaci kotun da ta raba auren nasu saboda rashin soyayya, sannan ta kuma roki kotun ta umurci mijinta da ya dauki nauyin kula da ‘ya’yansu.
Ahmed a martanin da ya mayar ya ce, Maryam ta gabatar da wasu bukatu daban-daban a kotu domin a raba aurensu, amma ba za ta iya raba shi da ‘ya’yansu ba.
“Ina rokon kotu da ta amince da bukatarta, amma ta bar min ‘ya’yana.
Rahoto: Kamal Aliyu Sabongida.