Daga Kamal Aliyu Sabon gida
Bamu Da masaniya kan shirin da CBN ke yi na sake fasalin Naira, sai dai mun ji a kafafen yada labarai, inji Ministan Kudi.
“Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmad, ta nesanta ma’aikatarta daga shirin babban bankin Najeriya CBN na sake fasalin kudin kasar Naira.”
“Ministan wanda ta yi tsokaci game da manufar a matsayin martani ga tambayar da Sanata Opeyemi Bamidele (APC Ekiti ta tsakiya) ya yi a yayin zaman kare kasafin kudin shekarar 2023 da kwamitin majalisar dattijai kan harkokin kudi, ya gargadi CBN kan illar da ka iya tasowa daga sabuwar manufar.
“Sanata Bamidele ya shaida wa ministan cewa bayan kwanaki biyu da bayyana shirin, ana samun tasirin darajar Naira da dalar Amurka.
“Kwana biyu kacal da bayyana wannan manufa, darajar Naira zuwa dalar Amurka ta tashi daga N740 zuwa N788, sakamakon yadda ake yin musanya da kudaden Naira na kudaden waje, musamman daloli.
Da take mayar da martani cikin gaggawa, ministar ta ce ita da ma’aikatarta ba su san da manufar ba sai dai kawai ta ji ta kafafen yada labarai.
“Ya ku ‘yan majalisar dattawa, CBN ba ta tuntube mu a ma’aikatar kudi kan shirin sake fasalin Naira ba kuma ba za mu iya cewa komai dangane da cancanta ko akasin haka ba.
“Duk da haka a matsayin dan Najeriya da ke da gatan kasancewa a kan gaba a harkokin kasafin kudin Najeriya, manufar da aka fitar a wannan lokaci tana nuna mummunar illa kan darajar Naira ga sauran kudaden kasashen waje.
“Duk da haka, zan yi kira ga wannan kwamiti da ya gayyaci gwamnan CBN don samun cikakken bayani game da cancantar manufofin da aka tsara da kuma daidai ko kuma aiwatar da shi a yanzu,” in ji ta.
Gwamnan babban bankin kasa, Godwin Emefiele, a ranar Larabar da ta gabata ya bayyana cewa babban bankin zai sauya fasalin kudin kasar daga N200 zuwa N1000.
Ya ce an dauki matakin ne domin ganin an shawo kan kudaden da ke yawo, kamar yadda ya bayyana cewa kashi 80 cikin 100 na kudaden kasar nan a wajen bankuna ne, kuma CBN ba zai bari lamarin ya ci gaba ba.”