Motar Dangote Ta Murkushe Wasu Jami’an Yan Sanda Har Lahira.
Wani hatsarin mota da ya afku a jihar Ogun ya yi sanadiyar mutuwar jami’in dan sanda da wasu mutane.
Kakakin hukumar FRSC a jihar, Florence Okpe ce ta tabbatar da haka a ranar Laraba 17 ga watn Mayu.
Ta ce hatsarin ya rutsa da babbar motar kamfanin Dangote ne inda direban ya gagara shawo kan motar.
Wata babbar mota ta kamfanin Dangote ta murkushe wani jami’in dan sanda har lahira akan hanyar Abeokuta zuwa Lagos a jihar Ogun.
Kakakin Hukumar Kula da Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) a jihar, Florence Okpe ce ta tabbatar da haka a wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba 17 ga watan Mayu.
Hukumar ta ce akalla mutane biyar ne suka samu raunuka a hatsarin da ya faru a ranar Talata da dare, cewar jaridar Punch.
Kakakin hukumar ta yi karin bayani akan hatsarin ta ce motocin da suka rutsa a hatsarin akwai motoci tara da babbar motar kamfanin Dangote da kuma motar diban kasa da bas da Toyota da sauransu.
Ta kara da cewa mutanen da hatsarin ya rutsa dasu sun hada da maza 7 da mace daya, Okpe ta ce mutum daya daga ciki ya mutu yayin da aka ceto mutane biyu ba tare da sunji wani ciwo ba.
Ya tabbatar cewa hatsarin ya faru ne dalilin gudu mai tsanani da direban babbar motan Dangote ke yi yayin da motar tafi karfinshi ya banke wasu motci kafin ya fada cikin kogi.
Mota kirar Toyota ta kama da wuta kafin daga bisani aka yi nasarar kashe gobarar da abin kashe gobara da aka samu daga gidan mai dake kusa, cewar jaridar Daily Post.
“Wadanda suka ji rauni an dauke su zuwa babban asibitin Ota don kula da lafiyarsu, daya daga cikinsu wanda aka tabbatar jami’in dan sanda ne a bakin aiki ya samu rauni bayan an kaishi asibitin daga bisani ya rasu,”
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim