Gobara ta kone wata makarantar firamare ta Tsangaya dake kauyen Kiyawa a karamar hukumar Bagwai a jihar Kano.
Da yake bayyana hakan a ranar Litinin, jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi, ya bayyana cewa hukumar kashe gobara ta Bichi ta samu kiran gaggawa daga Alhaji Ghadafi Sani Bagwai.
A cewarsa, gobarar ta lalata gaba daya ajujuwa goma sha hudu, ofisoshi goma sha biyu da bandaki ashirin da daya dake cikin harabar makarantar.
Da isar su wurin da lamarin ya faru, tawagar ceto ta gano cewa wani gini da aka yi amfani da shi a matsayin makarantar kwana ta Tsangaya ya kone da wuta.
Ya kuma bayyana cewa gobarar ta tashi ne daga babban ginin da ke gudanar da aikin bayar da na’urar hasken rana ta samu matsala ta kuma bazu zuwa wasu sassan makarantar Tsangayan.
Sai dai ya ce babu wani rai da aka rasa a lokacin wannan mummunan lamari domin an samu nasarar kwashe dukkan daliban.
Don haka Abdullahi ya jaddada kudirin hukumar na kare rayuka da dukiyoyin mazauna Kano.
Rahoto Kamal Aliyu Sabongida.