Muna bukatar Biliyan 869 Don Gudanar Da kidayar jama’a daga yan Najeriya – Gwamantin Tarayya.
Gwamnatin tarayya na neman tallafi daga ‘yan Najeriya domin gudanar da kidayar jama’a da gidaje a shekarar 2023 wadda ta ce za ta ci makudan kudade har naira biliyan 869.
Karamin ministan kasafin kudi da tsare-tsare na kasa, Clement Agba, wanda ya bayyana hakan a wani taron hadin gwiwa da aka yi a Abuja jiya, ya ce gwamnatin tarayya ta samar da kashi 46 na kasafin kudin.
Agba ya ce akwai sauran zunzurutun kudi har Naira biliyan 327.2 da ake bukata domin gudanar da kidayar yadda ya kamata.
Ya ce: “Abubuwan da ake bukata na wannan kidayar, ciki har da ayyukan da aka yi bayan kidayar, sun kai Naira biliyan 869, wannan kusan dala biliyan 1.88 ne.