Muna Da Haƙƙin Mallakar Muhalli Domin Gudanar Da Rayuwarmu –Almajiran Shaikh Zakzaky a Zariya
Daga Muhammad A. Dalhatu
Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky da aka fi sani da ‘yan shi’a a garin Zariya sun tashi cikin jimamin rushe musu makarantu da hukumar tsara birane ta jihar Kaduna wato KASUPDA tare da gamayyar jami’an tsaro suka yi a daren ranar Litinin.
Shaikh Abdulhamid Bello, wanda ya kasance shi ne wakilin ‘yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Zakzaky na garin Zariya da kewaye shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da ya kira a ranar Talatar 23 ga watan Mayun 2023 a daya daga cikin muhallin da aka rusa musu wanda ke Babban Dodo a cikin garin Zariya.
Shaikh Abdulhamid Bello ya ce gwamnatin ta Kaduna a karkashin El-Rufai ta rusa musu makarantu guda uku a Zariyan da ya hada da makarantun dake Babban Dodo Zariya da na Dogarawa a Sabon Garin Zariya da kuma na Samaru.
Shaikh Abdulhamid Bello ya fara ne da cewa; “makasudin kiran wannan taro domin gabatar da bayanai na gaggawa bisa ga abubuwan da suke faruwa ko kuma suka faru suna ma kan faruwa a wannan gari na Zariya ko ma na ce a jihar Kaduna gaba daya.
“Kamar yadda ‘yan’uwa musamman ‘yan jarida suka sani tun wancan makon an samu wata takarda da ta fito daga bangaren ma’aikatar tsare gine-gine wato KASUPDA na cewa akwai wasu wurare da za su yi rusau. Duk da mun dauki matakai na kalubalantar wannan har zuwa kotu da sauran su haka sai dai kawai muka ga kwatsam ana cikin wannan jimamin sai suka fara wannan rusau kwana biyu a Kaduna, sannan kuma jiya da daddare karfe 1 da kwata na dare suka dira”, ya labarta.
Ya ci gaba da cewa; “wannan makaranta ta Fudiyyah Babban Dodo Zariya sun taba rusata, to amma dai ba a fasa yin karatu a cikinta ba. Jiya da daddare suka zo kamar yadda kuke gani suka kara zubar da ginin wucin gadin da aka maida. To wannan ba su tsaya a nan ba, suka wuce kuma wata makaranta irin makamancin wannan a Dogarawa dake Sabon Garin Zariya suka rusata. Suka kuma wuce irin makamanciyarta dake Samaru suka rusa”, ya tabbatar.
Shehin Malamin ya ce a yayin rushe musu makaranta a Samarun Zariya, jami’an tsaron sun yi harbe-harbe inda suka harbi “‘yan’uwanmu har guda biyu yanzu suna asibiti”, in ji shi.
Malamin ya kara da cewa; “a nan ma sun yi harbi, amma ba su harbi kowa ba. Sun firgita mutanen gari da harbe-harbe. Jiya kusan dai ba a samu baccin kirki a nan cikin gari ba da kuma can Dogarawa da kuma Samaru, sun tada ma al’umma hankali”.
Ya yi kira ga al’umma da su fahimci cewa wannan abin da ake musu ta’addanci ne kuma zalunci ne. “Kuma shiru da zalunci idan ana yinsa kamar yarda da shi ne. Shiyasa dole ainihin al’umma mu tashi mu nema ma kawukanmu hakkokinmu”, ya lurantar.
“Idan mutum ya saurari jawabin da wani wai Kakakin KASUPDA ya fadi wai ko mutum yana da izini na mallakar gida suna da dama saboda wasu ‘yan dalilai na tsaro wanda bai bayyanar da dalilai na tsaron ba suna iya zuwa su rusa muhalli. Ban san lokacin da KASUPDA suka zama masu tabbatar da tsaro a cikin al’umma ba?’ ya tambaya.
Ya kara da cewa; “Sannan kuma a zo gidan mutum, ko muhallin da mutane ke karatu a zo kawai ba notis a shiga a rusa kamar yadda ake yi a wannan jiha, ban taba ganin irin wannan ba. An yi wadannan abubuwa tun cikin shekaru takwas din nan na mulkin wannan El-Rufai, amma kuma al’umma kamar ba su dauki mataki akansa ba”.
Ya yi tir da allawadai da rushe-rushen da aka yi musu inda ya ce ba su yarda ba. “Kuma wannan abin ba zai hana ya zama mu ci gaba da rayuwa ba. Tunda idan dai ba zai zo ya dauki rayuwarmu. Za mu rayu ne ‘ya’yanmu ba za su yi karatu ba? Za mu rayu ne ba za mu mallaki gidajen da zamu zauna a ciki ba?”, ya tambaya.
“Daga cikin irin karin rahotannin da muke samu shi ne akwai wasu gidajen daidaikun da suke son su kara rusawa a rubuce. Daga cikin gine-ginen da suka ce za su rusa guda 48, to idan ni dan shi’a ne shi ke nan ba ni da ‘yancin na mallaki gida? A dokar Nijeriya ko a dokar jihar Kaduna? Banda ‘yancin na rayuwa, banda ‘yancin na mallaki makaranta bisa ka’idoji da dokokin jiha da dokokin kasa don ba a sona ba a son a akidata, ba a son abin da nake yi?”, ya sake tambaya.
Ya ci gaba da cewa; “Wannan yakamata mutane su sa hankali su fahimci cewa abin da ake yi din nan, abu ne da ya sabawa hankali, ya sabawa doka, ya sabawa ka’idar addini baki daya”.
Ya ce babu wata takarda da suka bayar na cewa za su yi rusau kawai sun zo ne suka fara rushe-rushen. “Ko wancan takardar a cikin asiri aka samo ta na cewa za a yi rushe-rushe wanda har aka buga a jarida. Amma su aika cewa za su zo ko ku kau da kayanku ko kun yi laifi kaza bisa ga wannan za mu rusa muku muhallinku babu wannan”.
Ya ce a yanzu matakin da za su dauka shi ne na zuwa kotu; “Dokar da suka kafa su suke sabawa, amma za mu bi ko su aiwatar ko kar su aiwatar, mun yi wannan. Yanzu na farko mu tara ku nan muna son a isar mana da wannan sakon muna son duniya ta san wannan zaluncin da ta’addancin. Sannan akwai matakai daban-daban. Muna kuma addu’a Allah ta’ala tunda dai wani ya zalunci wani yana ganin yana da karfi, to akwai wani wanda ya fi shi karfi. Akwai kuma matakin zuwa shari’a domin isar da kokenmu”, ya ƙarƙare.