Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taya kungiyar kwallon kafa ta ƙasar Morocco, Atlas Loins murnar samun nasarar zuwa wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya da ake yi a Qatar 2022, yana mai cewa ƙungiyar na iya lashe gasar.
A wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Malam Garba Shehu, ya fitar, shugaban ya kuma yaba wa shugabannin ƙasar nan, musamman Sarki Mohammed na VI, da suka taka rawar a zo a gani, wanda a halin yanzu ya baiwa ɗaukacin Afrika fatan kowace kasa. a Nahiyar na iya lashe kofin FIFA da ake fata.
“Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taya tawagar kwallon kafar Morocco, Atlas Lions, da mai mulkin ƙasar, Sarki Mohammed na VI murnar kafa tarihi inda suka zama tawaga ta hudu daga wata kasa ta Afrika da ta taba tsallakewa zuwa zagayen kwata fainal na gasar cin kofin duniya, da kuma na farko da ya lashe matsayi a wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya ta FIFA Qatar 2022.
“Shugaba Buhari ya ce ƙasar Maroko ta sanya daukacin kasashen nahiyar alfahari da kwazon su, tare da ba da begen cewa tabbas ƙungiyar Afrika za ta iya lashe gasar, kuma ya kamata ta lashe gasar cin kofin duniya da ake yi a Qatar.
“Shugaba Buhari ya yabawa ƙungiyar bisa kwarewa da aikin haɗin gwiwa da suka yi, tare da lura da cewa ba za a iya cimma hakan ba sai da rawar da mahukuntan kasar Morocco suka taka wajen haɗa wata gaggarumar tawagar,” in ji sanarwar. godiya
Rahoto Shamsu S Abbakar Mairiga.