Wani iyali mai mutum shida sun mutu bayan da sukaci abinci da tsaka a ciki ta unguwar Mowe da ke karamar hukumar Obafemi Owode a jihar Ogun.
Waɗanda suka mutu sun haɗa da Adeleke John Samuel, wani akawun hayar, matarsa, Pamela Adeleke, ƴaƴansu biyu da wasu ƴan uwansu biyu, an gano gawarwakinsu ne da sanyin safiyar Juma’a, kamar yadda rahoton jaridar ALFIJIR HAUSA ya bayyana.
Rahoton ya kara da cewa lamarin ya faru ne a lokacin da Lawal Ojo, mai gadin kofar su ya yi zargin cewa ba a saba yin shiru a gidan da tsakar rana ba.
“Ya sanar da makwabtan da suka kutsa cikin gidan sai kawai suka gano gawarwakin waɗanda abin ya shafa a dakuma daban-daban,” in ji rahoton
Rahoto Shamsu S Abubakar Mairiga.