Okuneye Idris Olarenwaju wanda aka fi sani da Bobrisky ya fusata kan yadda mutane ke ɗaukar jinsinsa a ɗa namiji.
Shahararren ɗan wasan kwaikwayon mata da kuma yi kamar ɗiya mace, Bob ya bayyana irin gajiyar da yake fuskanta wajen shawo kan ƴan Najeriya game da zama yarinya.
A cewar Bob, irin wannan tattaunawa da ke da nasaba da hujjar jinsin wani tana faruwa ne kawai a Najeriya.
“Na ce ni yarinya ce har yanzu wasu suna shakka takuƙa a Nijeriya.
A ranar 30 ga Yuli, 2022, Bob a cikin wani sakon Instagram, ya caccaki maza yayin da yake nuna godiya game da rashin kasancewa ɗaya daga cikinsu.
Bob ya mayar da martani a fusace kan wani mutum da suka rabu da budurwarsa kuma ya sanar da aurensa ta hanyar Snapchat.
“To idan nine na ƙarshe zan godewa Allah da bai barni na ƙarasa da irin wannan wawancin ba. babu abinda za’a faɗa.
“Wannan jarumtaka ce a gare ni kuma har yanzu ina ba da hakuri kan girman kai.
“Koda yaushe maza za su tozarta. da Irin wannan wawan jinsi. Na gode Allah da na bar kungiyar,” in ji sakon.
Ganin yadda Bob ya sauya kamaninsa zuwa matakin sufan da mata ya jawo cece ku ce a Nijeriya, duba ga yadda inda ya saba harka da su su suna masa kallo a matsayin mace amma banda Nijeriya duk a cewarsa.
A halin yanzu ya cigaba da nuna alhininsa kan irin wanna batutuwan na al’umma da ke bayyanawa duniya cewa, shi namijine, ya kuma yi kira da kakkausar murya cewa a daina haɗasa da jinsin maza domin shi bana namiji bane tsaleliyar yarinyace na gani na faɗa duk a cewarsa.
Daga Shamsu A Abubakar Mairiga.