Mutumin da ke da mata 15 da yara 107 ya ce yana bukatar karin Mata.
Wani mutum mai suna David Sakayo Kaluhana dan garin Malava mai mata 15 ya bayyana cewa ya fi marfin ya tsaya da mata guda daya
Mutumin mai shekaru 63 da haihuwa kuma mai ‘ya’ya 107 ya ce ya tabbatar da cewa matansa ba sa kishi tsakaninsu ta hanyar boye yadda yake mu’amala da su
Lokacin da fitacciyar kafar yada labarai ta kasar Kenya, TUKO.co.ke ta ziyarci gidansa, matansa da ke a gidaje daban-daban sun fito don basu bayanai
Wani mutum mai shekaru 63, David Sakayo Kaluhana, mai mata 15, ya bayyana cewa suna zaune cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.
Mutumin wanda masanin tarihi ne, kuma mahaifi ga yara har guda 107 ya ce ya yanke shawarar auren mata da yawa ne saboda ya fi karfin zama da mace ɗaya.
Mutumin ya shaidawa shahararriyar kafar yada labarai ta Kenya, TUKO.co.ke, cewa yana tabbatar da cewa ya ciyar da iyalansa dukkansu, wato yaransa da matansa 15 da ke a gidaje daban-daban a kauyen.
Kaluhana ya kara da cewa yana da wasu matan a kasar dake makwaftaka da kasar ta Kenya wato Uganda, kuma ya ce har yanzu bai ma gama ba.
A cewarsa kari na nan tafe, ban gama ba haka nan. Ba zan iya bayyana lokacin da zan daina ba, amma nasan cewa muddin ana ba su abinda ya kamata, to fa ba za su yi korafi ba.”
A yayin da ake hirar, matan su kuma suna zauna tare suna ta hira cikin raha a tsakaninsu. Babbar matarsa tana da shekaru 60 a duniya.
Kaluhana ya kuma bayyana cewa matansa sun aminta da irin rayuwar da suke yi a karkashinsa. Kasancewar shi ne ke basu duk abinda suke bukata, ya ce yana kokarin yi wa kowace abinda ya kamata.
Ya ce matarsa ta farko tana da shekaru 49, sannan kuma karamar cikinsu tana da shekaru 23 ne.
Ya kara da cewa matarsa da ta fi yawan ‘ya’ya itace mai ‘ya’ya 16, a yayinda karamar ke da guda 5, wacce a haka ita ce mai yara kadan. Ya kuma ce har yanzu bai gama haihuwa ba, yana da sauran yara masu zuwa a gaba.
Sai dai Kaluhana ya bayyana cewa wasu daga cikin matan nasa su biyu sun rabu da shi saboda ba za su iya zaman auren ba.
Ya ce suna tsammanin zai rika zuwa wajensu kowane dare wanda hakan ba mai yiwu bane a tsarin da yake yi da sauran matan.
Matan sun bayyana cewa babu batun kishi a tsakaninsu, sun ce sun riga da sun shagaltu da renon yaransu.
Sannan wasu daga cikinsu sun bayyana cewa babu dalilin da zai sa su tsaya suna kishi tunda dai mijin nasu ya raba musu guraren da za su rika yin noma.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim