Na Dade Ina Sana’ar Motoci Motocin Da Aka Kwashe Mani Ni Nasayosu Daga Amurka.
Na sayi wadannan motocin ne kafin na zama Gwamna, tsohon Gwamnar zamfara Matawalle.
Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce yawancin motocin da jami’an tsaro suka kwashe daga gidajen sa guda biyu da ke Gusau da Maradun, an sayo su ne kafin ya zama gwamna.
Ya ce ba a ba shi kwafin umarnin kotu ba wanda ya baiwa jami’an tsaro damar mamaye gidansa kamar yadda magajinsa Dauda Lawal ya yi ikirari.
Na dade ina sana’ar mota kuma akasarin motocin jami’an tsaro da aka kama daga gidajena biyu, wadanda na siyo daga Amurka tun kafin na zama gwamna,” in ji tsohon gwamnan.
Ya ce wasu daga cikin motocin da aka tsare a gidansa da ke Maradun, masu hannu da shuni ne suka bayar da su, kuma dukkansu suna dauke da hotunan shugaba Tinubu da kansa.
“Motocin da suka kama a Maradun, wadanda masu hannu da shuni ne suka ba ni gudummuwa, kuma duk suna dauke da hotona da na Bola Ahmed Tinubu. Amma abin mamaki sai suka ce motocin na gwamnatin jihar ne,” inji shi.