Na Nemi da kotu data raba aurenmu saboda yawan kusantata da Mijina ke yi – Uwargida.
Wata mata mai suna Oluwatoyin Falade ta roki kotu da ta raba aurensu da mijinta saboda tsananin bin mata da yake.
Oluwatoyin mai shekaru 44 ta ce sun shafe shekaru fiye da 11 suna zaune amma ta gaji da zama da shi.
Mijin mai suna Segun ya amsa dukkan laifukan da ake tuhumarsa kuma ya yi alkawarin gyara halayensa.
Wata mata mai suna Oluwatoyin Falade a ranar Laraba ta roki kotu da ta raba aurensu da mijinta Segun saboda yawan neman mata da yake yi.
Oluwatoyin mai shekaru 44 ta ce sun shafe shekaru 11 suna zaman aure kuma Allah ya azurtasu da ‘ya’ya biyu da mijin nata.
Ma’auratan na rayuwa ne unguwar Tunde Davids dake Agege cikin jihar Lagos, cewar jaridar Premium Times.
“Mijina manemin mata ne duk inda ya hango mace, to hankalinsa zai karkata gare ta.
“Ina da ‘ya’ya mata biyu kafin na aure shi masu shekaru 11 da 18, muna rayuwa dasu amma ban yarda da mijina ba saboda yana da son mata.”
Ta kara da cewa mijina ya na sauya mata a duk lokacin da yaga dama kuma ba ya mutunta ni a matsayin mata, idan har kotu ba ta raba auren ba, ni zan gudu da ‘ya’ya na.”
Rahotanni sun tattaro matar na cewa makwabtansu har dariya suke saboda sanin halin mijinta na son mata.
Matar ta ce na gaji da zama dashi, Segun ba zai sauya ba, kullum halinsa kawai bin mata ne mai karar ta kara da cewa mijin nata ba ya kula da ‘ya’yansu.
Martanin mijin akan tuhumar da kotun ke yi akansa da yake mai da martani, Segun mai shekaru 46 ya amsa duk laifukan da ake tuhumarsa akansu.
A cewar mijin da zan yi karya ba, ina kawo mata gidannan amma nayi alkawari zan gyara halaye na, ina rokonta yafiya.”
“Kamar yadda kuke gani matata bul-bul take alaman ba ta shan wahala, kwanan nan na siya mata wayar tafi da gidanka kuma ina biyan kudin makarantar yara.”
Segun ya yi alkawarin gyara halayensa yayin da ya roki kotun ta kara ba shi dama saboda bai shirya rabuwa da matar ba.
Alkalin kotun, Mista Adewale Adegoke ya dage sauraran karar har zuwa ranar 30 ga watan Mayu don samun daidaito a tsakaninsu.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.