Na Rasa dangina saboda na auri wani dan Najeriya, yar Afirka ta kudu ta koka.
Wata Mata Mai ‘ya’ya Hudu Ta Bayyana Cewa Ta Rasa Danginta Saboda Aure Wani Dan Nijeriya.
Wata mutuniyar kasar Afrika ta kudu ta magantu kan yadda aurenta da dan Nijeriya ya shafi alakarta da yan uwanta
Uwar ‘ya’yan hudun ta rasa danginta amma ta yi ikirarin cewa sun yi kokarin kashe mata aure ne
Ta aika gagarumin sako ga mazan kasarta game da yan Nijeriya yayin da mutane da dama suka yi martani ga wallafarta
A cewarta, sun nemi taimakon jama’a sannan suka tsara labaran kanzon kurege don ganin sun rasa damar kula da yaransu.
Sai dai kuma, matar yar kasar Afrika ta kudu, ta nuna soyayyarta ga mijinta dan Nijeriya sannan ta shawarci mutanen Afrika ta Kudu da su daina kyamar yan Nijeriya.
Ta bayyana cewa ba dukka yan Nijeriya bane miyagu sannan ta kara da cewar kimanin shekaru 10 kenan da suka yi gwagwarmayar da danginta.
martani jama’a
@Yvonne Maqhula ta ce:
“Ki ji daɗin aurenki kin ji sannan ki so mijinki, wadanda ke jiranki ki dawo da kuka za su yi ta jira har sai idanunsu sun zama ja.”
@user5324279836152 ya ce:
“Duk kasashe suna da mutanen kirki da ba banza. ki yi addu’an samun nagari. ki mallaki mutumin sannan ki yi farin ciki.”
@user4618599173526 ya ce:
“Magana ta gaskiya tun da har dan Najeriya ya auri yar Afrika ta kudu ba karamin kokari ya yi ba fa saboda yawancin mazan Najeriya ba za su aikata haka ba.”
“A kodayaushe ina fadama mutane cewa ina da abokai yan Najeriya wadanda suka cika da soyayya kuma idan kana tare da su za ka ji kana da kariya amma wasu mutane sun tsane su.”
@Vic ta ce:
“Duk daya suke amma ina maki fatan alkhairi ina dai fatan kin ziyarci Najeriya ba wai kawai ki tsaya a nan Afrika ta kudu ba,,,ki ziyarci danginsa.”
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.