Shugaba Mohammadu Buhari ya ce Najeriya na binciken makamashin nukiliya domin samar da wutar lantarki.
Ya kuma bayyana ƙudurin gwamnatinsa na haɗa karfi da karfe ta hanyar mallakar makamashin nukiliya.
Shugaban ya yi jawabi ne a taron ministocin ƙasa da kasa kan makamashin nukiliya da aka kammala a karni na 21 da aka kammala a birnin Washington DC.
A cewarsa, gwamnatin tarayya ta fara aiki da hukumar kula da makamashin nukiliya ta Najeriya, NAEC, a matsayin hukumar da ke da alhakin samar da tsari da hanyoyin fasaha don ganowa, amfani da makamashin “atomic” don aikace-aikacen zaman lafiya don ci gaban zamantakewa da tattalin arziki na kasar.
Buhari Ya ce Najeriya ta kuma kafa Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Najeriya a matsayin wata hukuma mai zaman kanta ta gwamnati don tabbatar da tsaron lafiyar bil’adama da kare muhalli a fannin raya kasa, turawa da kuma amfani da makamashin nukiliya.
Buhari wanda ya yi magana ta bakin ministan kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire, Sanata. Adeleke Mamora, yace kamar sauran ƙasashe a nahiyar, Najeriya mai yawan al’umma sama da miliyan 200, na fama da matsalar ƙarancin makamashi, wanda hakan ya sanya ta zama dole. gwamnati ta yi taka-tsan-tsan wajen duba wasu zabukan makamashi wadanda suke da araha, masu kare muhalli da ɗorewa.
Saboda haka, ya bayyana cewa Najeriya ta ɗauki matakin yin cikakken bincike da kuma amfani da albarkatun makamashin nukiliya don samar da wutar lantarki, wanda zai ba da gudummawa ga tsaron makamashin kasar ta hanyar hada-hadar makamashin da ta dace..