Najeriya Ta Kasance Na 3 Cikin Jerin Kasashe 10 Da Aka Fi Kamawa Da Laifin Jamba.
Daga Al-Asad Al-Amin Funtua
Najeriya ta kasance a matsayi na uku a cikin manyan kasashe 10 da aka fi samun rahoton aikata laifukan zambar sana’a a cikin shekarar 2022.
Wannan dai ya zo ne a wani sabon bincike da Proxyrack ya gudanar, inda ya bayyana cewa kasar ta biyo bayan kasar Amurka mai mutane 625 masu laifukan zamba a duniya yayin da Afrika ta Kudu ta zo ta biyu da mutane 188 da suka aikata laifukan zamba sai Najeriya mai mutane 61.
Kamfanin da ke binciken alkaluman zamba, a cikin rahoton sa na zamba a masana’antu, ya bayyana cewa sassa daban-daban na ayyuka sun yi asarar dala biliyan 3.6 a duniya a cikin 2022 kadai, saboda karuwar ayyukan zamba cikin ‘yan shekarun nan.
A cewar rahoton, laifukan zamba da aka samu daga Najeriya na da alaka da banki, inda ya kara da cewa masana’antar sufuri da ma’ajiyar kaya ce ke kan gaba a cikin wannan jerin sassan da ke da karuwar ta’addanci a duniya.
Jerin kasashen 10 da suka fi yawan laifuffukan zamar masana’antu a duniya:
(1) Amurka mai mutane 625
(2) Afrika ta Kudu mai mutane 188
(3) Najeriya mai mutane 61
(4) Dubai mai mutane 60
(5) Canada mai mutane 50
(6) Kenya mai mutane 49
(7) Austaraliya mai mutane 38
(8) China mai mutane 33
(9) Saudiyya mai mutane 29
(10) Girka mai mutane 27