Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu, ya yi kira ga al’ummar jihar Bayelsa da su zabe shi a zabe mai zuwa na 2023, inda ya ce ya san hanyar da kasar za ta samu cigaba.
Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Alhamis din da ta gabata a wajen taron gangamin shugaban kasa na jam’iyyar APC da aka gudanar a Ox-Bow Lake Pavilion, Yenagoa, cikin tsauraran matakan tsaro.
Taron ya gudana ne a gaban majalisar sarakunan gargajiya ta jihar Bayelsa, karkashin jagorancin sarkin masarautar Ekpetiama, Sarki Bubaraye Dakolo.
Ɗan takarar jam’iyyar APC a lokacin da yake jawabi ga dimbin magoya bayansa, ya ce, “su biyo shi; ya san hanyar wadata. Su biyo shi, zai kai su can. A zabe shi; Zai kyautata rayuwar ƴan Nijeriya.
Tinubu yace Ku je Legas ku ga abin da muka yi, Tinubu ya fara yakin neman zaben Amurka da Turai ranar 4 ga watan Disamba.
Ya cigaba da cewa, Ceton su yana nan. wadata yana nan. Za su samar da dubban ayyuka. Bayelsa na daya daga cikin jahohin da suka fi yin sana’o’i, da albarkar ma’adinai, Zai mai da Bayelsa cibiyar fasaha da samar da guraben ayyukan yi duk inji shi.
Darakta-Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Simon Lalong, ya ce, “Za su yi nasara a ko’ina a Kudu maso Kudu Asiwaju zai yi nasara; shi naku ne.
A nasu jawabin, tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, sun bayyana cewa, Tinubu yana da kwazo, jajircewa, da kuma amana wajen tafiyar da mulkin Najeriya.
Rahoto: Salman Ibrahim Ɗan-ma’azu Katsina.