Nasha Da Kyar A Sakateriyar PDP – Wike
Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nwesom Wike ya bayyana irin kalubalen da rinka gamuwa da su a siyasa wadanda bai taba fadawa kowa ba
Wike ya bayyana haka ne yayin bikin godiya na musamman da aka shirya dominsa bayan kammala gwamnatinsa tare da mika mulki lafiya
Tsohon gwamnan ya bayyana yadda aka zuba masa guba da ya kusa kawo karshen rayuwarsa a watan Disamba na shekarar 2018
Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya bayyana yadda aka saka masa guba a sakatariyar jam’iyyar PDP a watan Disamba na shekarar 2018.
Wike ya bayyana haka ne yayin bikin godiya na musamman da aka shirya masa a St. Deanery a karamar hukumarObio-Akpor da ke jihar.
Ya ce gubar ta ratsa dukkan sassan jikinsa tare da kawo matsala a hanta da kuma kodarsa inda ya ce idan ba ikon Allah ba da ya mutu, cewar Daily Trust.
Wike ya ce a dalilin gubar har kodarsa da hantarsa sun samu matsala
A cewarsa a shekarar 2018, rana ta karshe a matsayina na shugaban ma’aikata, yayin bikin godiya, tun daga rana Lahadi a wancan lokacin ban fito daga dakina ba.
“Wadanda suka halarci wannan bikin sun sani ban yi bayani ba, na zauna ne kawai na fadawa mataimakin gwamna ya yi bayani a madadi na, na dauka daga ranar shikenan.”
Wike ya ce an dauke shi zuwa asibiti a Lebanon yayin da likitoci suka yi gwaje-gwaje suka tabbatar cewa hantarsa da koda duk sun bar aiki.
Ya bayyana cewa a lokacin zargin kowa yake yi inda ya yanke shawarar ba zai sake zuwa wani taro ba musamman a lokutan yakin neman zabensa, Daily Postta tattaro.
Tsohon gwamnan har ila yau, ya bayyana wani lokaci kuma da ubangiji ya kare shi da wasu shugabanni guda uku daga hadarin jirgin sama.
Ya kara da cewa bayan mintuna 15 da fara tafiya, sai muka ji karar inji ya fashe, daya daga cikin matukan jirgin ya ce ba matsala zamu iya komawa Port Harcourt lafiya, haka muka samu muka isa cikin dar-dar, ubangiji ya taimaka, babu wanda na fadawa.”
Ya ce yana boye irin wadannan munanan abubuwa da suka faru da shi don kada ya tayarwa magoya bayansa hankali don gudun yadda za su kasance.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.