Nayi Abinda Ya dace, Tinubu Ya Kare Cire Tallafin Mai
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kare matakin da ya dauka na cire tallafin man fetur, yana mai cewa an yi abin da ya dace.
Tinubu dai a lokacin rantsar da shi a matsayin shugaban kasa ya sanar da kawo karshen tallafin man fetur.
Daraktan yada labarai na fadar Villa, Abiodun Oladunjoye, ya ruwaito shugaban kasar ya bayyana haka a ranar Juma’a a wani taro da majalisar sarakunan Najeriya (NCTRN) a Aso Rock.
Ya kuma bayyana tallafin a matsayin giwa da ka iya durkusar da kasar nan domin tana fama da matsalar biyan albashi.
Shugaban ya ce bai kamata Najeriya ta zama Uban Kirsimeti ga kasashen da ke kusa ba ta hanyar ba su tallafin man fetur.
“Na gode da kuka mai da hankali ga abin da nake yi. Kun kula da cire tallafin. Me ya sa ya kamata mu kasance cikin zuciya mai kyau, mu ciyar da masu fasa kauri kuma mu zama Uban Kirsimeti ga ƙasashe maƙwabta, ko da yake sun ce ba kowace rana ce Kirsimeti ba?
“Giwar da za ta durkusar da Najeriya ita ce tallafin. Ƙasar da ba za ta iya biyan albashi ba kuma mun ce muna da damar ƙarfafa kanmu. Ina ganin mun yi abin da ya dace.”
Shugaban, ya ce gwamnatinsa za ta saurari shawarwari
“Dukkanmu kunnuwa ne. A shirye muke mu saurara a kowane lokaci. Na yi muku alƙawarin tsarin buɗe kofa kuma haka zan bi. Wannan manufar bude kofa ita ce ku kira ni kuma ku aiko mini a kowane lokaci duk wata damuwa da kuke da ita.
“Watakila ba za mu samu daidai kashi 100 na lokaci ba amma dole ne mu samu kashi 90 cikin 100 na lokacin kasar nan,” in ji shi.
Rahoto: Kamal Aliyu Sabongida