Nayi mafarki na auri shugaba Buhari meye fassaran mafarkina_inji wata budurwa.
Kamar yadda kuka sani mafarki wani abune mai ban al’ajabi, saboda wani lokaci idan akayi yana iya tabbata gaskiya.
Domin zaka iya ganin abin a zahiri ya faru wato zaka iya ganin faruwan abinda kayi mafarki a zahiri.
Yayin da wani lokacin yakan zamo kanzon kurege, inda yawan mafarke-mafarken da al’umma keyi a yayin da suke gudanar da bacci karyane ba gaskiya ba.
Wata budurwa mai suna Fatima ta bayyanawa duniya cewa, itafa tayi mafarkin cewa ta auri shugaban nijeriya Muhammadu buhari aure irinna sunna.
Budurwan mai suna Fatima ta bayyana hakane a shafinta na fasbuk.
Budurwan ta bayyana cewa, tashiga halin damuwa da rudani game da wannan mafarki nata inda tage neman al’umman musulmi da su temake ta su bayyana mata fassaran wannan mafarki nata kodan tasamu nutsuwa.
Rahoto Hajiya Msriya Azare.