NCCC ta bukaci a binciki shugaban EFCC kan Zargin cin hanci da rashawa da ake Masa.
Kungiyar North Central Citizens Council (NCCC) ta yi kira da ayi cikakken buncike akan zargin da ake yiwa Abdurrashid Bawa, shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa.
Kungiyar ta ce rayuwa mai tsada da Abdurrashid Bawa yake yi, na cigaba da jawo zargi akan hanyoyin samun kudin shugaban na hukumar EFCC.
Yayin ganawa da ‘yan jarida a Abuja, shugaban kungiyar (NCCC) Kwamared Muhammad Eneji yace babban dalilin kafa hukumar EFCC shine ta bunciki laifuffuka da suka shafi cin hanci da rashawa, da ta’adin dukiyar al’umma, wannan makasudin na samun tawaya ainun a karkashin shugaban hukumar na yanzu.
“Manyan gidajen jaridu na ciki da wajen kasar nan, sun sha kawo rahotannin zargin almubazzaranci da dukiyar al’umma da ake yiwa shugaban hukumar na yanzu”
“Daya daga cikin zarge-zargen da ake yiwa shugaban hukumar na kwanan nan shine yanda ya kashe makudan kudade har Dalar Amurka $300,000 (Dai-dai da Naira miliyan ashirin da biyu da dubu dari biyar) a hotal da sauran bukatu, a ziyarar da yakai Makka shi da iyalin sa a lokacin aikin Umra, adadin kudin da sun fi karfin albashin sa nesa ba kusa ba a matsayin sa na ma’aikacin gwamnati.
Hakanan kuma, ‘yan Nigeria ba zasu manta da badakalar kisan Abel Isah ba, wanda ma’aikacin damara ne na hukumar EFCC a Sokoto, rahotanni sun tabbatar an yi ta dukkan sa ne har ya mutu, saboda kin sa hannu da yayi akan wasu takardu masu lam’a. Duk kiraye-kirayen da aka ta yiwa hukumar kan ta bunciki lamarin abin ya ci tura. Kawo yanzu babu wata alama da ta nuna hukumar na da niyyar aiwatar da bincike kan lamarin, kamar yanda doka ta bata dama.