Daga Hajiya Mariya Azare.
Wata budurwa mabiya addinin kirista ta bayyana wasu muhimman dabi’u da ta koya agun musulmai.
Budurwan mai suna Gayobi Achawa, ta saka a shafinta na tiktok cewa, ita ba musulma bace amma tana da ‘yan uwa musulmai a cikin danginta.don haka a nan ne ma ta kuyi wasu halayya nasu gwanin birgewa inji ta.
Gayobi tace_mata musulmai suna nuna mana cewa basai mace tayi shigan banza ba, kafin kyawunta ya bayyana, Mata musulmai zasu rufe jikinsu amma zakaga kyawunsu ya bayyana.
Biyayya mata musulmai nada matukar biyayya kan addinin su. Babu musulmin dazai bari a taba martaban Al’Qur’ani da kuma martaban Manzon Allah S.A.W,
Musulmai ba munafukai bane, musulmai babu ruwansu da munafunci idan sukace zasuyi abu to lallai gaskiyan kenan zasuyi.