Ni da Wike kaman ‘Yan biyu ne, muna tsage gaskiya komai dacin ta’ – El-Rufai
Gwamnan Kaduna mai barin gado, Nasir El-Rufai ya jinjina wa gwamnan Ribas Nysome Wike bisa halartar taron kaddamar da littafi da dan jarida Emmanuel Ado ya buga.
Taron da ya samu halarcin gwamnan Ribas, Nysome Wike, Price Arthur Eze, Sarkin Zazzau Maimartaba Ahmed Bamalli, an gudanar da shi ne a dakin taro na Umaru Musa Yar’Adua dake Kaduna ranar Asabar.
A wurin taron Wike ya ce a kasar nan babu kamar gwamna Nasir El-Rufai.
” El-Rufai Jarumi ne wanda baya jin tsoron kowa. Dalili kuwa shine gwamna daya tilo da ya fito a 2017, ya tunatar da shugaban kasa alkawuran da ya dauka a lokacin kamfen ga talakawa. Ya ce akwai alamun gwamnati a lokacin tana kauce wa daga manufofin ta na gyaran kasa. Babu wanda zai iya fuskantar shugaban kasa haka gar da gar haka ya gaya masa irin wannan magana in ba jarumi ba.
“Bayannan ku duba irin ayyukan da ya rangada a jihar Kaduna sannan kuma da irin wadanda yayi a lokacin da yake Ministan Abuja. Haka sai irin su gwamna Nasir El-Rufai.
Bayan ya kaddamar da na shi gudunmawar har naira miliyan 20, Wike ya kara da yin kira ga wadanda ke adawa da zabin yan takarar shugabancin majalisa da jam’iyyar APC ta yi da su mai da wukaken su su bi umarnin jam’iyyar, ” Yin haka shine alheri musu, indan sun sani.”
A Jamwabin sa, gwamnan El-Rufai ya godewa gwamna Wike bisa kalaman karamci da yayi a kan sa inda ya kara da cewa shima Wiken ya gogarman aiki ne jarumi kuma mai tsage gaskiya komai dacin ta.
” Kai ma Wike ai jarumi ne, kuma gogarman aiki, ba ka tsoron tsage gaskiya komai dacinta, abinda yayi ka shi yayi ni wajen rangadawa talakawa aiki da fadin gaskiya tangararyarta. Nagoda da karamci matuka.
Bayan haka El-Rufai ya kara da cewa zai ci gaba da yin abin da ya dace daga nan har zuwa ranar 29 ga Mayu, ranar da zai mika ragamar mulki ga Sanata Uba Sani.
” Zan ci gaba da fatattakar baragurbin ma’aikata a jihar Kaduna, sannan duk ginin da ba a yi shi daidai ba kamar yadda doka ta ce, ya mu rusa su da nan har bu bar gwamnati. Za mu yi haka ne saboda gwamnati mai zuwa ba sai ta maimaita abin da muka yi ba.
Shi kuma gwamna mai jiran Kado, Uba Sani, wanda babban kai ne a wurin taron ya yaba da ayyukan da gwamna El-Rufa yi a tsawon mulkin sa yana mai cewa samun irin su El-Rufai dace ne.
Wakilin Tinubu taron, Kashim Imam, ya mika sakon zababben shugaban kasa Bola Tinubu ga baki masu halartar taro kamar haka.
In ka ba El-Rufai kowani irin aiki, Zai gama da shi kamar yankan wuka” In ji Tinubu.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim