Nijeriya Ta Biya Bashin Tiriliyoyin Kuɗaɗen da Taci Daga Waje, Ta Sake Runtumo Bashi
Gwamntin Nijeriya ta yi nasarar biyan bashin N3.63trn da bankin duniya da sauran waɗanda suka ba ƙasar rance ke binta
Waɗanda suka ba Nijeriya rance sun karbi waɗannan kuɗaɗen ne tsakanin watan Janairu zuwa Disamban 2022 da a gabata
Duk da cewa biyan bashin labari ne dai madadi, amma gwamnati ta sake runtumo wasu tiriliyoyin kuɗin da suka kusan ninka wanda ta biya
A cewar rahoton ofishin kula da bashi (DMO) da ALFIJIR HAUSA ta samo, Nijeriya ta kashe N3.63trn wajen biyan bashin waje da na cikin gida a shekarar 2022 da ta gabata.
Waɗanda suka samu nasarar samun biyan bashin sun haɗa da gwamnatin China, bankin Muslunci, bankin Larabawa, hukumar ba da lamuni ta duniya da dai sauransu.
Duba ga alkaluman hukumar DMO, Nijeriya ta yi amfani da farashin 448.08 wajen biyan bashin dala 2.40bn, wanda ya yi daidai da N1.07trn.
A bangare guda, ta biya bashin cikin gida da ya kai N2.56trn, kamar yadda rahoton ya bayyana.
Kuɗaɗen cikin gida da Nijeriya ta biya sun haɗa da masu zuba hannun jari, bankuna da dai sauran wadanda aka ci kuɗaɗensu.
DMO ta bayyana cewa, adadin kuɗaɗen da aka kashe wajen biyan bashi a watan Afrilun 2022 bai haura 529.88bn ba.
Adadin kuɗaɗen da aka biya a kowane wata a rancen cikin gida
A kasa mun tattaro jerin kuɗaɗen da aka biya a kowane wata daga asusun gwamnati a 2022.
Janairu – N188.36bn
Faburairu – N103.88bn
Maris – N376.44bn
Afrilu – N529.88bn
Mayu – N66.97bn
Yuni – N67.88bn
Yuli – N248.72bn
Agusta – N152.44bn
Satumba – N419.42bn
Oktoba – N302.42bn
Nuwamba – N57.24bn
Disamba – N47.11bn
Rancen kasashen waje da Najeriya ta biya
China – $256,583,866.48
International Monetary Fund – $14,908,327.22
African Development Bank – $114,170,633.49
International Fund For Agricultural Development – $6,364,700.31
African Development Fund – $29,287,792.35
Africa Growing Together Fund – $389,139.37
International Development Association – $446,064,137.09
European Development Fund – $5,243,339.76
Arab Bank for Economic Development in Africa – $632,181.86
Islamic Development Bank – $1,552,989.77
India – $8,166,901.40
France – $46,825,104.25
Germany – $24,978,907.67
A baya dama rahoto ya bayyana adadin kasahsne da ke bin Najeriya bashi mai yawan gaske a shekarar 2022.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim