Yadda ake cigaba da samun masu digiri a Nijeriya amma basu iya rubutu ba ko kaɗan bare karatu.
Yawancin ‘yan nijeriya da suka kammala karatun digiri magana da rubutu da turanci yanayi musu wahala.
Mataimakin shugaban jami’an Godfrey Okoye da ke Enugu, farfesa Chiristian Anieke, yace magana da rubutun turanci kalubale ne ga dimbin ‘yan nijeriya da suka kammala karatun digiri.
Anieke yayi magana ne a lokacin da jami’an hukuman kula da jami’o’in kasan nan suka ziyaraci jami’an a ranan juma’a, kamfanin dillancin labaran nijeriya ya bayarda rahoton cewa jami’an NUC sun kasance a cibiyan don tantance shirye-shiryenta na digiri.
Anieke yace, hukuman ta GOUNI ta gano amfanin da turancin a matsayin babban rauni ga dimbin daliban da suka kammala karatu daga wasu cibiyoyi, inda ya bayyana cewa, wasu daliban da suka kammala karatun digiri na farko suna shan wahalan rubutu ko karatu da turanci daidai.
Wannan shine dalilin da yasa muka bullo da wani kwas mai suna Comminication in English, kuma rashin iyawan dalibai nayin amfani da harshen ingilishi daidai yana iya zama saboda asalinsu.
Rahoto Hajiya Mariya Azare.