NNPC Ya Tura Sako Ga Yan Nijeriya Bayan Tinubu Ya Cire Tallafin Man Fetur
Shugaban kamfanin NNPC ya ce matakin da Bola Tinubu ya dauka na cire tallafin mai ya yi dai-dai kuma suna goyon baya
Kyari ya bayyana haka ne a wani taron gaggawa don mai da martani akan cire tallafin da Shugaba Tinubu ya yi a bikin rantsarwa
Mele Kyari ya ba da tabbacin kamfanin na da wadataccen mai da zai biya bukatun ‘yan Najeriya har na tsawon wata daya a kasar
Kamfanin Mai ta Najeriya (NNPC) ya goyi bayan cire tallafin mai da Shugaba Bola Tinubu ya yi lokacin da ya ke jawabi a bikin rantsar da shi a ranar Litinin 29 ga watan Mayu.
Tinubu ya bayyana cire tallafin ne a bikin rantsar da shi inda ya ce ya cire ne saboda kasafin kudin shekarar 2023 bai ba da gurbin tallafin mai ba.
Da yake jawabi a taron gaggawa a Abuja, shugaban kamfanin NNPC, Mele Kyari ya ce cire tallafin an yi shi ne saboda ci gaban kamfanin, cewar gidan talabijin na Channels.
Kyari ya kara da cewa kamfanin ya na kashe makudan kudade daga cikin ribar da suke samu don biyan kudin tallafin.
Kyari ya ce suna da isasshen mai da zai wadaci ‘yan Najeriya
Ya kara da cewa bai kamata mutane su tsorata su fara layi a gidajen mai ba don siyan mai da yawa saboda su boye, cewar rahotanni.
Ya ce suna da wadataccen mai a kamfaninsu da zai wadaci ‘yan Najeriya har na tsawon wata daya, yayin da yace suna kula da samarwa da kuma rarraba mai din a fadin kasar.
Mele Kyari ya tabbatar da goyon bayansa akan matakin da Shugaba Bola Tinubu ya dauka akan cire tallafin yayin da ya tabbatar wa ‘yan Najeriya wadatuwar mai din a fadin kasar ganin yadda aka fara layi a gidajen mai.
Ba sabon abu bane a ga ‘yan Najeriya sun cika gidajen mai domin sayen mai a bangarori daban-daban na kasar.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim