Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta ce amincewa da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, da kungiyar tuntuba ta shugabannin Arewa ta Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara ta yi, aiki ne na kutsa kai.
Ta ce amincewa da hakan wata dabara ce da abokan hamayyarta na siyasa ke yi don kawar da dan takararta na shugaban kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso daga aikin ceto kasar nan daga kangin talauci.
Jam’iyyar NNPP ta ki amincewa da tantance Dogara da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Babachir Lawal, na cewa ba ta da abin da ake bukata na lashe zaben shugaban kasa da tafiyar da kasar.
A cikin sanarwar da Farfesa Doknan Sheni da tsohon ministan albarkatun ruwa, Mukhtari Shehu Shagari suka fitar, kungiyar tuntuba ta shugabannin Arewa ta amince da Atiku.
Sai dai da yake zantawa da manema labarai jiya, shugaban NNPP na kasa Farfesa Ahmed Rufa’i Alkali ya ce: “Muna farin cikin sanar da ku cewa a cikin ‘yan watannin da suka gabata jam’iyyar NNPP ta bunkasa daga karfi zuwa karfi, inda ta janyo hankulan ‘yan Najeriya masu kima. mun kuma kara samun tallafin jama’a a duk fadin kasar…
“Yunkurin kawar da hankalin dan takararmu na shugaban kasa ya dauki salo da dama, tun daga kan karyar da ake yi na cewa yana cikin takara a matsayin sa na dan takara, a lokacin da waccan labarin karya ya ci tura, sai suka ce yana cikin takarar raba kuri’u na dan takararsu. …
“Na baya-bayan nan a kokarin karkatar da dan takararmu na shugaban kasa shine ‘yardar da dan takarar shugaban kasa da wata kungiya da ke kiran kansu da kungiyar tuntuba ta shugabannin Arewa (NLCF).
“A matsayinmu na jam’iyyar siyasa da ta yi imani da ‘yancin dimokradiyya na mutane na goyon bayan dan takarar da suke so, haka nan hakkinmu ne kada a jawo mu cikin aikin da bai cancanta ba.
“A batun NNPP, kungiyar tuntuba ta shugabannin Arewa (NLCF) ba ta san mu ba, kuma ba a taba samun wata alaka da kungiyar ba.
“Gaskiya wasu ‘yan siyasa karkashin jagorancin tsohon shugaban majalisar wakilai Yakubu Dogara da tsohon SGF Babaachir Lawal sun zo wurinmu, a can baya a karkashin tutar addinin Kirista, suna ikirarin cewa jam’iyyarsu ta APC ta mayar da su saniyar ware.
“A wancan lokacin babu wanda ya taba ambaton mu da wata kungiya mai suna Dandalin shawarwarin shugabannin Arewa, domin duba da yadda muka lura da wasu abubuwa na rashin gaskiya a cikin ayyukansu, ga dukkan alamu sun zo NNPP ne a kan siyayya ta kansu, suna neman mafita da mafaka.
“Domin Yakubu Dogara da abokan tafiyarsa su juyo suna zargin jam’iyyarmu da dan takararmu na shugaban kasa da cewa ba su yi wa ‘yan Najeriya karya ba ‘shirin aikinsu na kwanaki 90 a zabe’ ya nuna karara cewa kungiyar na kokarin ganin an riga an yanke hukunci.
Rahoto: Kamal Aliyu Sabongida