Karban Bashin Fa Ya Isa Haka, Ofishin Tattalin Basussuka DMO Ya Gargadi Gwamnatin Buhari.
Kawo yanzu ana bin Najeriya bashin N42.8 trillion; N26.2 trillion na gida, N16.6 trillion na waje.
Yanzu Najeriya na karɓan bashin kuɗaɗe don biyan tsaffin basussukan da aka karɓa a shekarun baya.
Gwamnatin tarayya ta ce karɓan basussukan sun zama wajibi ne saboda kuɗin shiga sun daina isa.
Ofishin Manejin basussukan Najeriya (DMO) ya bayyana cewa akwai buƙatar gaggawa na gwamnatin tarayya ta rage karɓan basussuka don a iya biyan na kasa.”
Dirakta Janar na ma’aikatar DMO, Patience Oniha, ta bayyana hakan ranar Alhamis a wani waksho da aka shiryawa yan majalisa, rahoton TheCable.
“Ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta nemo hanyar rage kashe kuɗi, samar da isassun kuɗin shiga sannan kuma a tabbatar bashin da za’a karɓa ayyuka za’a yi dasu wadanda ribar za’a samu da su zasu iya biyan bashin.”
”Tace yanzu basussukan gida da na waje sun yiwa Najeriya katutu kuma kudin ruwa na kara yawa, BusinessDay. ta ruwaito.
“A cewarta, Saboda haka ya kamata a rage karban bashi kuma a mayar da hankali kan samar da kudin shiga daga bangaren man fetur da sauransu.”
“Basussukan da ake bin Najeriya sun yi yawa a tsawon shekarun nan. Haka yasa kudin ruwan dake hawa na kara yawa.”
“Dogaro kan arzikin man fetur ke haddasa rashin samun isassun kudin shiga.”
“A cewarta, kawo watan Yuni 2022 dai ana bin Najeriya bashin N42.8 trillion (N26.2 trillion na gida, N16.6 trillion na waje).
Game da bashin da kasar Sin ke binmu kuwa, Oniha yace $3.6 billion ne kacal.
“Sauƙin abun shine bashin kasar Sin na aiki ne. Bamu dogara da shi ba. Bai da yawa amma saboda aiki ake da shi yana da kyau.”
Najeriya yanzu bashi muke karɓan don biyan wani bashin da akaci a baya.
A wani labarin kuwa, tsohon gwamnan bankin CBN kuma Sarkin Kano na 14, Sanusi Lamido Sanusi, ya bayyana cewa yanzu fa Najeriya bashi ake karba don biyan wani bashin.
Sanusi ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na tarawa jikoki da tattaba kunne bashi.
“Tsohon Sarkin yace Najeriya babu wani cigaba da take da alaman samu nangaba.
Daga Zuhair Ali Ibrahim.