Osinbajo Ya Shilla Sierre Lieone Domin Jagorantar Sa Ido A Kan Zabe.
Tsohon Mataimakin shugaban kasar Najeriya mai barin gado, Farfesa Yemi Osinbajo, na shirin isa kasar Saliyo a wannan Asabar din, domin jagorantar kungiyar kasashe masu sa ido a zaben kasar mai wakilai 12, COG.
LEADERSHIP ta rawaito cewa Osinbajo ya amince da tayin kungiyar Commonwealth domin jagorantar kungiyar sa ido da sakatariyarta Patricia Scotland ta kafa domin sa ido kan babban zaben kasar Saliyo.
Da yake tabbatar da tafiyar Osinbajo ta shafinsa na Twitter, mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Laolu Akande, ya ce tsohon mataimakin shugaban kasar zai kasance a Saliyo na tsawon wata guda.
Akande ya rubuta cewa: “Nan take tsohon mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya nufi kasar Saliyo a yau a matsayin shugaban kungiyar masu sa ido ta Commonwealth mai mutane 12 domin gudanar da zaben kasar. Zai yi magana da Latsa Conf. a ranar Litinin & kasance a cikin kasar don sauran wata. Daga baya, Osinbajo-COG zai bayar da rahoto kan sahihancin zabe.”
A cewar sakatariyar Commonwealth, Osinbajo zai hadu da wasu jiga-jigai daga bangarori daban-daban da suka hada da ‘yan siyasa, shari’a, kafafen yada labarai, kwararrun jinsi da kuma harkokin zabe na kasashen Commonwealth domin gudanar da wannan aiki.