Daga Kamal Aliyu Sabongida
Bayan rasuwar Ifeanyi, dan Afrobeats Davido, dan jam’iyyar PDP, jihar Osun ta dakatar da harkokin siyasa na tsawon mako guda.
Davido, wanda kani ne ga zababben gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya rasa dansa ne bayan nutsewar da ya yi a cikin ruwa.
Wata sanarwa da shugaban riko na jam’iyyar PDP na jihar Osun, Dr Adekunle Akindele, ya bayyana alhininsa game da faruwar lamarin tare da addu’ar Allah ya jikan su.
“Bayan rasuwar Ifeanyi, an dakatar da duk wasu ayyukan jam’iyyar don ta’aziyya ga iyalan Adeleke.
“Muna jimamin ficewar danmu Ifeanyi cikin bakin ciki. Muna addu’ar Allah ya jikan sa. Rana ce ta bakin ciki amma mun dage da imaninmu ga Ubangijin talikai.
“Ta’aziyyarmu tana zuwa ga Davido, jakadan matasanmu. Muna mika ta’aziyya ga mahaifinmu, Dokta Deji Adeleke da dukan dangin Adeleke. Muna addu’ar Ubangiji Allah ya baiwa iyalai ikon jure wannan rashin da ba za a iya gyarawa ba,” in ji sanarwar.