Daga Kamal Aliyu Sabongida
Babban jami’in kamfanin na NNPC, Mele Kyari ya ce ana yi wa rayuwarsa barazana saboda sauyin da ake samu a bangaren man fetur.
Mista Kyari ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Laraba a wajen taron tabbatar da gaskiya da rikon amana da majalisar wakilai ta shirya wanda kwamitin yaki da cin hanci da rashawa na majalisar wakilai.
Ya ce masu adawa da sauye-sauye a fannin sun yi ta yin barazana a yunkurinsu na ganin sun samu nasara.
“Ba tare da wasu kalmomi ba, ina so in ce wannan masana’antar tana kan kofa na canji, akwai gagarumin canji da ke faruwa kuma yana da tsada sosai kuma yana da tsada ga mutane da yawa ciki har da ni.
“Akwai barazanar rayuwa, zan iya faɗin haka, anyi ta barazanar kisa da yawa amma ba mu damu da wannan ba. Mun yi imani cewa babu mai mutuwa sai lokacinsa ne.
“Amma wannan shine farashin canji. Lokacin da mutane suka kaurace wa abin da suka saba zuwa wani sabon abu wanda zai dauke kimarsu kuma ya amfana da su, za su mayar da martani,” inji shi.