Cristiano Ronaldo Bazai Je Kungiyar Kwallon kafa ta Al-Nassari.
Dan wasan Kwallon kafa Cristiano Ronaldo ya karyata Jita Jita Da ake Yadawa na zuwan sa Kungiyar Kwallon kafa Ta Al-Nassari Dake Kasar Saudi Arabia .
Hakan Ya biyo Bayan Da Kungiyar Tayi Masa tayin Biyan Albashi Mafi Tsoka Da Babu Wanda ya taba daukarsa kimanin £200M da wasu doriya.
Dan wasan dai yanxu Yana Kasuwa ne Bayan Da Kungiyar Kwallon kafa Ta Manchester United ta kawo karshen kwantiragi a tsakanin su a watan data gabata.
Rahoto: Bashir Muhammad Maiwada.