“Cristiano Ronaldo” zai bar Kungiyar ƙwallon ƙafa na “Manchester United” bisa yarjejeniyar A tsakanin sa da ƙungiyar.
“ƙungiyar ta gode masa saboda gagarumar gudunmawar da ya bayar a tsawon lokuta biyu Na Kakar Wasanni ,2021, da 2022.
Ɗan Wasan Cristiano Ronaldo Ya bayyanan cewa, Bayan tattaunawa da Manchester United, mun amince da mu kawo karshen kwantiragin mu da gaggawa.”
Yace yana son “Manchester United” kuma yana son magoya bayanta, hakan ba zai taba canzawa ba a garesa, koda ya koma wata ƙungiyar taka ledan.”
“Tauraron ɗan wasan ƙwallon Ya ƙara da cewa Koyaya, yana jin kamar lokacin da ya dace da shi ne don neman sabon ƙalubale acikin aikinsa.
Ronaldo Ya Kuma Bayyana cewa
yana yiwa Manchester United fatan samun nasara a sauran kakar wasanni da kuma nan gaba.”
Daga Bashir Muhammad Maiwada.