Rundunar Sojin Kasar Na Sun Kwamishe Matasa Yan Kungiyar Maliyas A Maiduguri
Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar cafke matasa ‘yan kungiyar ‘Marlian Gang’ da suka addabi birnin Maiduguri
Matasan da ke kwaikwayar mawaki Naira Marley da ke Kudancin Najeriya suna kai hari akan mutane tare da kwace wayoyinsu
Rundunar ta kai samamen ne a yankunan bayan samun bayanan sirri da kuma korafi daga mutanen yankin
Rundunar sojin ‘Operatiin Hadin Kai’ ta yi nasarar kama wasu gungun masu tada zaune tsaye 15 da suka addabi birnin Maiduguri.
Samamen wanda aka gudanar a ranar Juma’a 9 ga watan Yuni a yankunan Gwange da Jajere da kuma Umarari da ke cikin birnin Maiduguri, ya sa an yi nasarar cafke matasan da dama.
Kafar Zagazola Makama da ke rahoto kan yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi ta tattaro cewa jami’an sojin sun kai samame ne bayan mazauna unguwannin Gwange da Umarari da Jajeri sun kai korafi akan lamarin.
Gungun matasan wanda aka fi sani da ‘Marlian Gang’ da ke danganta kansu da mawaki Azeez Fashola (Naira Marley), an kama su ne a ranar 9 ga watan Yuni da misalin karfe 11:40 na dare.
Rahoton ya bayyana cewa matasan na kai farmaki kan mutane da kuma kwace wayoyinsu da sauran kayayyaki masu amfani, cewar Tribune.
Ayyukan matasan ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane da dama da asarar dukiyoyi, yayin da aka samu wayoyin hannu da bindiga da wukake da gatari da sauransu.
Kafar Zagazola Kakama ta tabbatar cewa an mika matasan ga Hukumar’Yan Sandan cikin gida ta DSS don daukar mataki na gaba, cewar rahotanni.
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim