Rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom ta cafke mutane 15 bisa zargin faffasa bankuna.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Odiko MacDon ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Lahadi.
Ya ce, “Mun samu labarin cewa an kai wa wasu bankuna hari a karamar hukumar Oron kuma nan take ‘yan sanda suka kai dauki.
“Yayin da muke magana kimanin mutane 15 aka kama dangane da lamarin.
Wasu matasa a yankin sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadinsu kan karancin kudin Naira, a ranar Juma’a.
“Kwamishanan ‘yan sanda, Mista Olatoye Durosinmi ya bayyana bakin cikinsa game da lamarin, ya kuma umurci jami’an ‘yan sanda na shiyya-shiyya a kananan hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da cewa ba a sake samun tabarbarewar doka da oda ba.”
MacDon ya kara da cewa kwamishinan ya yi kira ga mazauna yankin da su kasance masu bin doka da oda domin duk wanda aka kama yana barnatar da dukiyoyin jama’a za a hukunta shi da gaske.
Ya ce rundunar ‘yan sanda za ta yi duk mai yiwuwa don ganin cewa Akwa Ibom ta kasance daya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Najeriya.
Tuni dai mazauna yankin ke fargabar kada a bude bankunan yankin a ranar Litinin bayan umarnin da kungiyar ma’aikatan bankin ta yi wa mambobinsu na kada su je aiki inda aka kai hare-hare kan cibiyoyin banki.
Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito, wata majiya a yankin ta ce akalla bankuna uku da ke kan titin Oron a karamar hukumar da wani dakin sanyi na wani dan majalisar dokokin kasar ne aka lalata a yayin zanga-zangar.
Rahoto: Shamsu S Abbakar Mairiga.