Sai na gama Ayyukan da Gwamna El rufa’i Ya faro kafin na faro nawa sabo ~Cewar Sanata Uba sani
Gabanin mika ragamar mulki a ranar 29 ga watan Mayu, zababben gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yi alkawarin kammala dukkan ayyukan da gwamnan jihar mai barin gado ya fara, daga nan kuma zai fara wasu sabbin ayyuka.
Uba Sani ya bayyana haka ne a ranar Asabar bayan Gwamnan El-Rufai ya mika masa rahoton kwamitin mika mulki a gidan gwamnatin Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna.
Yayin da yake yabawa gwamnan mai barin gado, ya ce zai yi nazarin rahoton tare da Neman shawarwari.
“Ina godiya ga shugabana kuma mai ba ni shawara, Gwamna Nasir el-Rufai. Tare da shi mun zabi tawagar da ta gabatar da rahoton kwamitin mika mulki. Zan yi nazarin rahoton kuma za mu aiwatar da mafi yawan wannan tsari domin a shekara ta A 2015, ba mu samu wannan damar ba. Za mu kammala dukkan abubuwan da Gwamna Nasir El-Rufai ya fara kuma za mu yi aiki kan wasu sabbin wurare ma.”
Tun da farko, gwamnan jihar Kaduna mai barin gado, Malam Nasir El-Rufai ne ya mika rahoton kwamitin mika mulki na 2023 ga zababben gwamnan jihar, Sanata Uba Sani.
Da yake jawabi yayin gabatar da rahoton, El-Rufai, wanda ya yaba wa kwamitin mika mulki, ya ce rahoton zai zama wani tsari da jagora ga gwamnatin mai jiran gado.
El-Rufai ya lura cewa a shekarar 2015 bayan ya kayar da abokin hamayyarsa kuma ya lashe zaben gwamna, babu rahoton mika mulki yayin da tawagarsa ta samar da nata rahoton mika mulki wanda ya aiwatar.
Gwamnan ya ce: “Ina godiya ga kwamitin mika mulki bisa ga kwazon da suka yi. Ba mu yi sa’a ba a shekarar 2015, mun fitar da rahoton mika mulki bayan mun ci zabe wanda ya zama tsari. Aikina na biyu shi ne mika kwafin rahoton kwamitin mika mulki ga zababben gwamna da mataimakinsa.
“Rahoton kwamitin mika mulki na 2015 ya yi aiki da gwamnatina a matsayin tsari kuma ina fata wannan rahoton zai zama wani tsari ga gwamnatin zababben gwamnan.”
Shima da yake nasa jawabin sakataren gwamnatin jihar Kaduna wanda shine shugaban kwamitin mika mulki na shekarar 2023, Alhaji Balarabe Abbas Lawal yace rahoton zai taimakawa gwamnatin Sanata Uba Sani mai jiran gado wajen ganin jihar Kaduna ta samu ci gaba.