Babban bankin najeriya CBN yayi gargadi a Abuja, a jiya talata.
Akan wadanda Suke wulakanta Naira Sun Cancanci Zuwa Gidan Yari, Da kuma matakin da naira ta taka, musamman a cikin taron mutane.
Wanda yayi hakan za a daureshi tsawon wata shidda a gidan yari, ko kuma fansar naira dubu hamsin (50,000).
Sashe na 21 a cikin na 3 na dokar CBN 2007, ya gabatar da cewa wulakanta naira laifine, kuma dolene a hukunta Wanda yayi.
Principal manager na sashen naira a CBN, Ms Ngozi Etim, tayi gargadin a lokacin da take magana da Kungiyar ‘yan jarida ta NAN.
Tace, babban bankin yana aiki da jami’an ‘yan Sanda, da ‘yan kwana- kwana, da EFCC.
CBN kuma yana aiki da ma’aikatan kudi na fararen kaya wato Nigerian Financial Intelligence Unit, domin a hukunta, masu cin mutuncin.
Tayi tsokaci akan sakin kudi a cikin mutane, inda takara da cewar tsarin yana nan a Matsayin Wanda yafi karbuwa a manufa. Kada a kuskura a cukwi kwuye kudi sai dai asa a anbulop.
Ba a yadda mai ya taba kudi ba, saidai ka ajesu cikin natsuwa a mutunce kamar yadda kake aje rigarka.
Bazaka taba yima rigarka dauda ba da kanka, kuma bazaka taba aje rigarka akasa ba. Dan haka akwai bukatar ka aje mamu naira a mutunce, kamar yadda tace.
Ta kara da cewa a dokar CBN ta bada damar a kama duk Wanda wulakanta naira.
Etim ta kara da cewa, naira tana nan a matsayin mai daraja a cikin kasar kuma dolene a ajeta a tsaftace kowane lokaci.
A cikin jawabin Darakta na CBN, Mr Osita Nwanisobi, shima ya gargadi ‘yan najeriya dasu yi amfani da naira cikin kulawa.
Akwai kesa- kesai dayawa wadanda Mutane suka ci mutuncin naira, suka wulakanta su a wurin partittika.
Kamar yadda wadannan Mutane sukayi, cikin daya kodai al’adace ba hujja bace da zaku wulakanta nairori.
Akwai bidiyoyi dayawa, wadanda suka hada da ‘yan siyasa yadda suke wulakanta naira.
Takaddun naira kuma sun zamo wani abu a gareji da wuraren aje motoci a kowane sashe na kasar, musamman a yayin yin wani biki ko taro.
Babban bankin ya bayyana duk Wanda ya ci mutuncin naira dolene a hukunta shi.
Rahoto Rafi’atu Mustapha Katsina.