Wani Jami”in Hukumar Shige Da Fice Ya Rasa Karin Girma Sakamakon Kai Karar Ogansa da yayi.w
Wani Jami”in Hukumar Shige Da Fice Ya Rasa Karin Girma Sakamakon Kai Karar Ogansa da yayi kan cin zarafinsa da yai.
Ana karaw masu ɗamara matsayi ko mukami duk bayan shekara biyu a Nijeriya wanda haka nada alaƙa karin albashinsu ma.
Karin girma dai a Nijeriya na zuwa a yawan shekarun da ka shafe a kana aiki, wato bayan shekara biyu ko uku-uku.
Wani jami’in hukumar kula da shige da fice ta kasa (NIS), Yemi Badru, da ake zargin wani babban jami’i, Nasir Umar ya ci zarafinsa a ranar 30 ga watan Yuli, 2019, ya koka kan hana shi jarabawar karin girma da hukumar ta yi saboda ya kai rahoton lamarin.
Badaru, wanda yake da matsayin mataimakin sufeto, ya yi zargin cewa Kwanturola Janar na NIS, Isa Idris, ya ki ba shi damar zana jarrabawar girma ta hukumar duk da cewa ya cancanta, wanda kuma ya ci ace ya samu karin girma har sau biyu tun bayan faruwar lamarin a shekarar 2019.
Badru yace: Hukuma ta ta yi alkawarin ba ni damar rubuta jarabawar karin girma, bayan da daya daga cikin jaridun kasar nan sun rubuta batu, amma daga baya an yi min barazanar kora daga aiki, idan ban janye karar dana shigar da Umar Nasir Mohammed ba, wanda yaci min zarafi.”
“Umar, wanda ya zage ni a bainar jama’a, amma kuma duk da haka aka ce a tuhume ni, kuma ya samu kariya da ga babbar shedikwata. Baya ma da kara masa girma da akai zuwa babban Sufeto. Ni kuma har yanzu ba’a bani damar sake rubuta jarrabawar karin girma a makon da ya gabata zuwa wani babban matsayi ba.”
Amma da yake mayar da martani, mai baiwa shugaban hukumar shuge da fice ta kasa shawara kan harkokin shari’a, Mallam Adamu, ya ce Badru, wanda ake zargin Umar ya ci zarafinsa, yana fuskantar kwamitin ladabtarwa kan wasu batutuwa da ba a bayyana ba.
Mai bashi shawarar ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da The Guardiana abuja kan batun Badru din
Adamu yace: A iya saninsa, Badru yana da shari’a a kansa har a kotuna guda uku; a babban kotun tarayya, Ikoyii da ke Legas; da Kotunan masana’antu dake, Abuja da Legas, kuma baya ga wadancan kararraki a gaban kotun, kuma yana fuskantar kwamitin ladabtarwa”.
Adamu ya kara da cewa, Idan mutum yana gaban kwamittin ladabtarwa ko kuma yana da kara a kotu, to hukumar mu tana yanke hukunci kan yayi jarabawa ko kuwa a’a. Sabida gudun kar a samu matsala lokacin da jarabawar ta fito ko hukumar ta yanke shawarar a sallameshi ma gaba daya. Sannan ita kanta hukumar ta yanke shawarar karbar duk wani hukunci da kwamitin ladabtarwa ya dauka.
Adamu ya karkare jawabinsa ga wakilin jaridar The Guardian da cewa Ba wanda ya hana Badru rubuta jarabawa, kawai dai abinda muka sani, shine yaki ya tsaya ya sauari hukuncin kwamitin ladabtarwa kafin a komai, yaje sai kai korafi yake gidajen jaridu”.
Daga Karshe Adamu Yace: A wajen mu, Badru ba shi da wata kara a kan Nasir Umar, su biyun suna da shari’a a gaban kotun ma’aikata kuma kwamitin ladabtarwa ya zauna ya ce su je su daidaita kansu, amma Badru ya ce an fifita Umar ba tare da hujja ba don tabbatar da zargin da yake yi.”
Rahoto Zuhair Ali Ibrahim.