Sarkin Hausawan Maraba ya koka na ganin samun baragurbi a kasuwar yan Lemu.
Akwai yan giya da yan kwaya a kasuwar yan lemu Maraba, Sarkin Hausawan Maraban Gurku.
A wani sautin murya da aka jiyo tsakanin wayar Sarkin Alhaji Usman Mani da Abdullahi Mai Gada, wanda aka jiyo muryan Shugaban Kasuwar ta yan lemu yana magana shima, Sarkin ya gargadi Ma’aikacin babbar kotu mai lamba ta uku watoh “High Court 3” a turance.
Sarkin ya nemi Abdullahi mai Gada ya baiwa Ma’aikacin kotun waya domin yayi magana dashi domin gudun kada ya dauki sautin muryansa inda nan take ya mikawa Dauda wayar, Sarki ya fara masa tambayoyi kan dalilin dayasa yazo kasuwar inda bayan ya fada masa, sai sarkin ya gar-gadeshi da cewa lallai yayi taka tsan-tsan da wannan Shari’ar ko kuma ya fadawa JIMO a dauke shi a maidashi kauye da aiki.