Wani ya lakaɗawa tsohuwar budurwar sa duka. saboda ta ƙi ta aure shi a Delta.
Ana zargin wani mutum mai suna Atumu Treasure Oluwa Benz Richer da dukan wata budurwarsa mai suna Peace saboda ta ƙi aurensa.
An bayyana cewa, masoyan na daban ne a watanni shida da suka gabata a garin Irri da ke karamar hukumar Isoko ta Kudu a jihar Delta.
A cewar wani mai fafutuka, Israel Joe, wanda ya bayyana labarin a shafinsa na Instagram, mutumin ya shiga gidan Peace, inda ya kulle kofa, ya fara dukanta da shaƙe ta saboda ta ƙi aurensa ranar Litinin.
Joe ya ce makwabta ne suka ji kukan matar, suka cece ta daga masoyinta da suka rabu kuma suka kama shi.
Ɗan gwagwarmayar ya ci gaba da tuhumar kwamishinan ƴan sandan jihar Delta, Ari Mohammed Ali, domin tabbatar da gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu, yana mai cewa ana tattaunawa a ofishin ƴan sanda na Oleh.
Rahoto: Shamsu S Abbakar Mairiga.