Daga Shamsu S Abbakar Mairiga.
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ce babu gudu babu ja da baya kan shirin sake fasalin takardun banki na N1,000, N500 da kuma N200, ya kara da cewa ba za a bar ƴan siyasa su hada kayan aiki da ƴan daba don tsoratar da masu zabe a babban zabe na 2023 ba.
Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a wata hira da yayi da shi a ƙasar Burtaniya bayan ya gana da mai martaba sarki Charles III a fadar Buckingham.
Buhari ya kuma ce babban bankin Najeriya (CBN) ya bai wa ƴan Najeriya isasshen lokacin da za su rika ajiye takardun kuɗi na Naira na yanzu a bankuna domin musanya sabbin wadanda aka yi wa kwaskwarima da za a fitar nan da ranar 15 ga Disamba, 2022.
“A kan wannan canjin kuɗi, za a samu kuɗi da yawa amma an bayar da lokaci daga Oktoba zuwa Disamba, watanni uku ya isa duk kuɗin da kake da shi, a canza shi ta hanyar doka.
“Don haka, ban san dalilin da yasa mutane ke korafi game da hakan ba,” in ji Shugaban.
Ya kuma ce manufar da Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya sanar a ranar 26 ga Oktoba, 2022 ta zo ta tsaya.
“Ba za a koma ba,” in ji Buhari game da shawarar sake fasalin takardun naira uku.
“Burina shine in tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun yarda cewa muna mutunta su a matsayin gwamnati.
“Don haka ‘yan Najeriya su zabi wanda suke so daga kowace jam’iyya ta siyasa. Ba za a bar kowa ya tattara kayan aiki da ’yan daba don tsoratar da mutane a kowace mazaba. Abin da nake so in shiga a tarihin Najeriya ke nan a matsayina na shugaba.”