Shugaba Tinubu Yana Ganawar Sirri Da Tsohon Sarkin Kano Sanusi A Fadar Gwamnatin Tarayya.
Daga Al-Asad Al-Amin Funtua
Tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, yana wata ganawar sirri da Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, a fadar gwamnati da ke Abuja.
Jaridar POLITICS NIGERIA, ta rawaito cewa Sanusi wanda ya taba rike mukamin gwamnan babban bankin ‘kasar ya isa fadar shugaban ‘kasar ne ‘yan mintuna kadan kafin karfe 5:00 na yamma.
Wannan ganawa dai na zuwa ne mako guda bayan da shugaba Tinubu ya dakatar da Godwin Emefiele, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya.
Duk da cewa ba a bayyana takamaiman bayanin tattaunawar ta su ba, amma abin lura shi ne ganawar tasu ta farko tun bayan da Tinubu ya hau kujerar shugaban ‘kasa a ranar 29 ga watan Mayu.
In bamu mantaba a kwanakin baya an yi ta yada jita-jita game da yiwuwar dawo da Sanusi a matsayin Sarkin Kano. Sai dai gwamnatin jahar mai ci ta yi watsi da wannan hasashe.